YADDA AKE SALLAH JANAZAH
Sallar Gawa (Sallar Janazah) dukkan Maluman Musulunci sunyi ittifaki akan cewa farillah ce ta kifayah wato wasu daga cikin al'ummah sukan iya dauke ma wasu.
Bayan kayi alwala tana da rukunai kamar haka :
1. NIYYAH : Zaka niyyaci yin sallah bisa wannan gawar. Furta niyyah ba wajibi bane. Domin ita niyyah a zuciya take.
2. TSAIWA : Dukkan Malaman Musulunci sun ce wajibi ne yinta atsaye. Bai halatta kayita azaune ko akan abin hawa ba. Sai dai in kana da larurar jinya da ta halatta maka yin haka.
3. KABBARORI HUDU : Wannan shine adadin da aka ruwaito mafi inganci daga Ma'abota ilimi daga Sahabbai da Tabi'ai. Kamar yadda Imamul Bukhariy da Muslim da Tirmidhiy suka ruwaito daga Sayyiduna Jabir bn Abdillahil Ansariy (ra) : yace "Lallai Manzon Allah (ﷺ) yayi ma Najjashiy sallah, kuma yayi kabbarori guda hudu.
An ruwaito ittifaki akan haka daga Manyan Maluman Fiqhu irin su Imamu Malik da Shafi'iy da Ahmad da Is'haq bn Rahawaihi da Sufyanuth Thawree, da Ibnul Mubarak (Allah ya jikansu).
4. CHIRA HANNU YAYIN KABBARA : Wannan a kabbarar farko ne kawai akeyi banda sauran kabbarorin domin ba'a ruwaito cewa Manzon Allah (ﷺ) yana cira hannu yayin wata kabbara asallar janazah ba, in banda ta farkon.
5. KARANTA FATIHA : Saboda hadisin da Imamul Bukhariy ya ruwaito daga Talha bn Abdillah yace "Nayi sallaci gawa abayan Abdullahi bn Abbas (ra) sai ya karanta fatiha, sannan yace "ITA TANA CIKIN SUNNAH".
Imamut Tirmidhiy ma ya ruwaito irinsa kuma yace Sashen Ma'abota ilimi daga Sahabbai da kuma wasunsu sun zabi aiki bisa wannan fahimtar, wato suna karanta fatiha bayan kabbarar farko asallar Janazah.
Yin salati bisa Manzon Allah (ﷺ) da kowacce sigah ko kuma nau'in salatin da ya sawwaqa agareka. Sai dai yafi kyau kayi wani daga cikin salatai da aka ruwaito sigoginsu daga Annabi (ﷺ) saboda dacewa da koyi.
6. YIN ADDU'A GA MAMACI : Shima rukuni ne saboda hadisin da Manzon Allah (ﷺ) yake cewa : "IDAN ZAKU SALLACI MAMACI TO KU TSARKAKE ADDU'A GARESHI".
(Abu Dawud da Baihaqiy da Ibnu Maajah da Ibnu Hibbaan ne suka ruwaitoshi kuma Ibnu Hibban ya ingantashi).
Zaka iya yin addu'a da duk sigar da ta sawwaka gareka. Amma dai anfi so kayi wata daga addu'o'in da aka ruwaito daga Manzon Allah (ﷺ).
Misali akwai riwayar Sayyiduna Abu Hurairah yace "Manzon Allah (saww) yayi addu'a a sallar Janazah yana cewa :
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺃﻧﺖ ﺭﺑﻬﺎ، ﻭﺃﻧﺖ ﺧﻠﻘﺘﻬﺎ ﻭﺃﻧﺖ ﺭﺯﻗﺘﻬﺎ ﻭﺃﻧﺖ ﻫﺪﻳﺘﻬﺎ ﻟﻺﺳﻼﻡ ﻭﺃﻧﺖ ﻗﺒﻀﺖ ﺭﻭﺣﻬﺎ ، ﻭﺃﻧﺖ ﺃﻋﻠﻢ ﺑﺴﺮﻫﺎ ﻭ ﻋﻼﻧﻴﺘﻬﺎ، ﺟﺌﻨﺎ ﺷﻔﻌﺎﺀ ﻟﻪ ﻓﺎﻏﻔﺮ ﻟﻪ ﺫﻧﺒﻪ .
Allahumma anta Rabbuha, Wa anta Khlaqtaha wa anta razaqtaha wa anta hadaitaha lil islami. Wa anta Qabadhta ruhaha, wa anta a'alamu bi sirriha wa alaniyatiha. Ji'ina shufa'a'a lahu fagfir Lahu.
- Aufu bn Malik (ra) yace : "Naji Manzon Allah (ﷺ) yana sallatar wata gawa yana cewa:
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻪ ﻭﺍﺭﺣﻤﻪ ﻭﺍﻋﻒ ﻋﻨﻪ ﻭﻋﺎﻓﻪ ﻭﺃﻛﺮﻡ ﻧﺰﻟﻪ ﻭﻭﺳﻊ ﻣﺪﺧﻠﻪ ﻭﺍﻏﺴﻠﻪ ﺑﻤﺂﺀ ﻭﺛﻠﺞ ﻭﺑﺮﺩ . ﻭﻧﻘﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﺨﻄﺎﻳﺎ ﻛﻤﺎ ﻳﻨﻘﻰ ﺍﻟﺜﻮﺏ ﺍﻷﺑﻴﺾ ﻣﻦ ﺍﻟﺪﻧﺲ ﻭﺃﺑﺪﻟﻪ ﺩﺍﺭﺍ ﺧﻴﺮﺍ ﻣﻦ ﺩﺍﺭﻩ ﻭﺃﻫﻼ ﺧﻴﺮﺍ ﻣﻦ ﺃﻫﻠﻪ ﻭﺯﻭﺟﺎ ﺧﻴﺮﺍ ﻣﻦ ﺯﻭﺟﻪ ﻭﻗﻪ ﻓﺘﻨﺔ ﺍﻟﻘﺒﺮ ﻭﻋﺬﺍﺏ ﺍﻟﻨﺎﺭ .
Shaikh Sayyid Sabiq acikin Fiqhus Sunnah yace azahiri mutum zai yi wadannan addu'o'in ne wadanda aka ruwaito daga Manzon Allah (saww) ba tare da chanza lafazi ko lamiri ba. Koda Mamacin nan Mace ne ko Namiji ne ko yaro. Domin Makomar addu'ar dai akan kalmar "Gawa" ne ko "MAMACI" wannan kuwa ba ya chanzuwa ko Mace ce ko namiji.
/7. ADDU'A BAYAN KABBARA TA HUDU : Shima rukuni ne saboda Hadisin da Imamu Ahmad ya ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi bn Abi Awfa (ra) cewa Wata 'yarsa ta rasu. Bayan yayi kabbarorin nan hudu, ya tsaya yana addu'a gwargwadon dadewar da yayi atsakanin sauran kabbarorin. Bayan ya idar sai yace musu "ANNABI (SAW) YA KASANCE YANA YIN HAKA A SALLAR JANAZAH".
Imam Shafi'iy yace addu'ar da za'a yi bayan kabbara ta hudu ita ce "Allahumma la tahrimna ajrahu wala taftinna ba'adahu".
'Dan gidan Abu Hurairah kuma yace "Magabata (wato sahabbai) sun kasance suna cewa "Allahumma rabbana aatina fid dunya hasanah wa dil Akhirati hasanah, wa Qinaa azaban naar".
8. SALLAMAH : Itama rukuni ce awajen dukkan Malaman Musulunci in banda Abu Haneefah shi awajensa wajibah ce.
Ko sallama daya ko biyu duk wacce mutum yayi ta isar masa. Amma dai Sahabbai azamaninsu duk sallama guda sukeyi.
{SIFFAR SALLAR}
Idan kai ne Limami Bayan kayi alwala, Idan Namiji ne zaka tsaya adaidai wajen kansa ne. Idan kuma mace ce zaka tsaya akan saitin wajen tsakiyarta ne.
Yayin da ka Qulla niyyarka Zaka 'daga hannu kayi kabbara. Sannan ka dora hannunka na dama akan na haggu bisa Qirjinka.
Sai ka karanta fatiha, Sannan kayi kabbara ta biyu. Sai kayi ma Annabi salati (ﷺ) sannan kayi kabbara ta uku.
Bayan kabbara ta uku sai kayi ma mamacin nan addu'a da irin sigogin da muka kawo abaya, ko kuma duk sigar da ta sawwaka agareka.
Sai kayi kabbara ta hudu.. Sannan ka Qara addu'a sannan kayi sallama.
Wasu daga Maluman Mazhabinmu na Malikiyyah sun ce ya halatta ka chanza lamirin zuwa na mace idan gawar Mace ce. Wato maimakon "LAHU" sai kace "LAHA". maimakon "HI" KO "HU" Sai kasa "HA".
Allah ya kyautata karshenmu yasa mu cika da imani ameeen.
[ JAN HANKALI]
Dan Allah jama'a adai na tafiya a nata hira ana shewa a hanyar tafiya makabarta ko aciki makabarta saboda abin da ake nema a wannan lokacin a ta nemarwa mutum gaffara shine yafi ba surutu ba.
Allah ya kyautata karshenmu yasa mu cika da imani ameeen.
daga dalibinku
musa s zage.
وبالله التوفيق
ALLAH YASAKA DA ALKAIRI SHEIKH
ReplyDeleteAMEEN ALHAJI
DeleteAmeen
ReplyDelete