Yan Najeriya Na Kokawa Kan Tsadar Wutar Lantarki Duk Da Karancinta.


 Yan Najeriya Na Ci Gaba Da Kokawa Kan Tsadar Wutar Lantarki Duk Da Karancinta.


Duk da karin kudin wutar lantarki da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi a farkon wannan shekarar da sama da kashi 160, don inganta yanayin samar da wutar, al’ummar kasar na korafi kan biyan makudan kudade, alhali kuwa ba sa samun wutar da suke bukata. 

Gwamnnatin Tarayyar Najeriya ta ce matsaloli masu tarin yawa ne suka haddasa karancin wutar lantarki da ake fuskanta a duk fadin kasar.

To sai dai ministan makamashi na kasar Abubakar Aliyu wanda ya sanar da hakan, ya ce yanzu haka gwamnati na iya kokarinta domin shawo kan lamarin.

Comments