TUSHEN ABINDA KE JANYO MATSALOLIN AURE A KASAR HAUSA.

 



 TUSHEN ABINDA KE JANYO MATSALOLIN AURE A KASAR HAUSA 


Topic : TUSHEN ABINDA KE JANYO MATSALOLIN AURE. 


Yau A Shirin namu na zamantakewa zamu tabo  maudu'in ne da ya shafi zamantakewar aure, Wanda suna taka nuhimmiyar rawa wajen rugujewar zamantakewar aure.



style="text-align: center;">            *Tushen matsalolin aure*             


1_Rashin tsoron Allah. 

A gaskiya a yanxu akwai karancin Rashin tsoron Allah cikin Al"umma Wanda ya hada har da cikin zamantakewar aure. Kuma ba Rashin ilimi bane ke haddasa hakan, a"a an sani ake take sanin ana biyewa son zuciya.


Mafi yawancin matsalolin aure suna farawa ne daga  bin son zuciya da yin abinda aka ga dama sabanin karantar war Allah da manzon sa bisa zamantakewar aure.

Da ma'aurata zamu ji tsoron Allah muyi biyayya ga tsarin Allah da manzon sa bisa zamantakewar aure, da dayawa daga cikin matsalolin aure sun kaura. 


2_Rashin sanin darajar auren kansa. 


Da yawa yanxu bamu mahimmanta aure Abinda aka fi bawa muhimmanci sune hidiman aure da sharholiyar da  ake yi a yanxu wajen biki.


Yakamata a daraja aure a muhimman tashi kada a dauke shi a aikin je ka nayi ka. Muna manta cewa addini ne Kuma ibada ce kuma Allah ya tsara Mana shi yanda zai kasance tun daga neman auren har yanda za ayi zamantakewar auren.

Amma Basu ne a gaban mu ba, shiyasa aure ya zama abinda ya zama a yau, mun bar unarnin Allah ta Yaya za muga yanda muke so?


3_Rashin sanin ilimin zamantakewar aure. 


Wannan gaba tana da muhimmanci gaske Wanda yakamata saurayi da budurwa su San ilimin zamantakewar aure kafin auren..

Wannan kalubale ne babba ga iyaye, musamman iyaye mata. Kullum mu siffantu da dabi"a mai kyau cikin zamantakewar auren mu sai yaran mu su yi koyi daga gare mu.


Mu koyawa yaran mu mata su San haqqoqin su Dana mazajensu a kan su, mu koya musu yanda zasu fahimci mazajensu su zauna da su cikin girmamawa da kyautatawa.

Haka nan yaran mu maza mu koyar dasu yanda zasu zama mazajen wasu Kuma iyayen wasu .

Don haka kafin kawaye su yiwa dayan mu hudubar sharri game da zamantakewar aure mu Karan kanmu mu dauki wannan ragamar. 


3_Rashin fahimtar  juna bayan aure. 


Fahimtar juna tsakanin ma'aurata Abu ne Mai matukar muhimmanci.

Yana da kyau ma'aurata su san junansu sosai.

Fannin dabi'un su,  fannin abin da Suka fi so da Wanda basu so,hakanan banbancin ra'ayin dake tsakanin su da samun daidaito, fannin Mai Suka fi so game da junan su.

Rashin fahimta na kawo matsala sosai a zamantakewar aure.



4_Rashin tsafta da gyaran jiki da iya Girki Mai dadi. 


Wannan gaba ma sai ma"aurata sun Kula sosai don samun nutsuwa tatattare da junan su.

Musamman mata, a ko da yaushe jikin mace nason Kula da gyara. Jiki mace na samun nakasu yayin da take haihuwa ko babu haihuwama. Ki Saba da gyaran jikin ki sosai domin shine jarinki , komai na jikin mace ado ne, Kuma an halicce su ne domin su burge mazajen nu da kuma burge su 

Idan mace Kuma ta zama ballagaza Bata damu ta gyara kanta ba, Tom da sannu zata  Fara fuskantar matsala a gidan auren ta.

Don haka mu Kula da tsaftar junan mu daga mazan har matan 👍👍

Sai mu samu soyayyar Mai tsaftar 💖💞💞. 


Presented by ummu walad. 

( Maman atifah)🖋

Post by msz hausa. 




Comments